1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TikTok zai kalubalanci dokar Amrika a gaban shari'a

April 25, 2024

Kamfanin TikTok ya yi barazanar yin fito na fito a gaban shari'a kan dokar Amirka na son janye kamfani daga zama mallakin kasar Chaina.

https://p.dw.com/p/4fA03
TikTok zai kalubalanci dokar Amrika a gaban shari'a
TikTok zai kalubalanci dokar Amrika a gaban shari'aHoto: Olivier Douliery/AFP

A ranar Laraba, Shugaba Joe Biden na Amirka ya sanya hannu kan dokar da ta bai wa mallakin kamfanin na ByteDance wa'adin watanni 9 ya siyar da TikoTok. Idan har kamfanin ByteDance ya ki siyar da TikTok, zai fuskanci hukuncin janye sa daga manhajojin Apple da kuma Google app store a Amirkar.

Karin bayani:Amirka ta dakatar da manhajar TikTok da WeChat

Ana kuma sa ran masu amfanin da Manhajar TikTok a Amirka miliyan 170 su dauki matakin shari'a kan wannan doka. A watan Nuwanbar 2022 ce dai, wani alkalin Kotun Montana da hana hukuncin haramta TikTok a kasar. Haka zalika a baya wata kotu ta dakatar da tsohon shugaban kasar Donald Trump daga haramta manhajar.