1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta dakatar da manhajar TikTok da WeChat

Binta Aliyu Zurmi
September 18, 2020

Sashin kula da huldar cinikayyar kasar Amirka ya dakatar da manhajar Tiktok da WeChat na kamfanonin kasar China.

https://p.dw.com/p/3ihLD
USA TikTok Bürogebäude in Kalifornien
Hoto: Getty Images/M. Tama

Amirka na zargin wadannan manhajojin da bada bayanan shirri na masu amfani da su ga kasar ta Sin wanda suka ce hakan na zama barazana ga harkar tsaro da ma tatalin arzikin kasar.

Daga ranar Lahadin da ke tafe duk wanda ke Amirka ba za iya saka manhajojin a wayarsa ba, amma wadanda suka dade da manhajar za su ci gaba da amfani sai dai ba zasu sami damar samu sauyi ba a duk lokacin da aka samu wani sabon abu.

Kamfanonin sun bayyana cewar kasar Amirka na zama guda daga cikin manyan kasuwanninsu wanda suke da sama da miliyan dari da ke amfani da su.

Tun bayan da aka fara samun rade-radin Amirka za ta dakatar da wadannan manhajojin, shugaban kanfanin Tiktok Kevin Mayer ya ajiye mukaminsa.