1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta sake samun tallafin tsaro daga Rasha

May 5, 2024

Kasar Rasha ta aika wa Nijar sabbin masu bayar da shawara kan harkokin tsaro da ma kayan yaki, yayin da Nijar ke neman dakarun Amirka kimanin 1,000 su fice daga kasar.

https://p.dw.com/p/4fWQI
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

Rahotanni sun yi nuni da cewa tawagar farko ta mashawarta kan sha'anin tsaro 10 sun isa kasar ne a ranar 10 ga watan Afrilun 2024 tare da wasu na'urorin tsaro na sama. Ko a ranar Asabar wasu manyan jiragen yaki biyu sun isa kasar. A yanzu Rasha ta turo wa Nijar jiragen saman dakon kaya na yaki guda uku dauke da kayayyakin yaki da kuma masu horo.

Karin bayani:Sojojin Rasha sun canji na Amurka a Nijar

A ranar Alhamis din da ta gabata ce dai, sakataren tsaron Amirka Lloyd Austin ya ce an Rasha ta girki dakarunta a wani sasanin soji da ke kusa da filin jirgim sama na Yammai, inda nan ma akwai dakarun Amirka.

Tun bayan da sojoji suka kwace mulki da kasar a shekarar 2023, Nijar ta kori dakarun Faransa da ke zama uwargijiyarta tare da datse yarjejeniyar tsaro tsakaninta da Amirka.