1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Rasha jibge a wani sansanin soji a Yamai

Abdourahamane Hassane
May 3, 2024

Ministan tsaron na Amurka Lioyd Austin ya ce sojojin Rasha na jibge a wani sansanin sojin sama a Nijar wanda kuma ke dauke da sojojin Amurka, bayan Yamai ta bukaci janye sojojin Amurka daga kasar.

https://p.dw.com/p/4fUjy
Hoto: DW

Sojoji na Rashana cikin sansanin sojin sama na rudunar mai numba 101 da ke kusa da filin saukar jiragen saman kasa da kasa da ke a birnin Yamai. Sojojin Rashar na cikin wani gini gwa da gwa da sojojin Amurka, sai dai akwai shinge a tsakaninsu. Aikewa da sojojin Rasha zuwa sansanin sojin sama da ke a birnin Yaman, ya sanya sojojin Rasha da na Amurka kusa da juna,a daidai lokacin da Washington da Moscow ke cikin tsaka mai wuya dangane da yakin Ukraine.