1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ECOWAS ta bukaci a saki Bazoum da iyalansa

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 15, 2023

Kotun kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, ta bukaci sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar da su saki shugaban kasar da suka kifar da Mohamed Bazoum da iyalansa.

https://p.dw.com/p/4aDgp
Nijar | Juyin Mulki | Sojoji | Mohamed Bazoum | ECOWAS | CEDEAO
Mohamed Bazoum da iyalansa na dab da samun 'yanci, bayan umurnin kotu na sakin suHoto: Evelyn Hockstein/Pool/File Photo/REUTERS

Da yake yanke hukunci kan ci gaba da tsare Mohamed Bazoum din da iyalansa tun bayan hambarar da gwamnatinsa, alkalin kotun mai shari'a Gberi-Be Ouattara ya bukaci sojojin su gaggauta sakin sa ba tare da wani sharadi ba kana su mayar da doka da oda a kasar ta hanyar mika mulkin ga hannun wanda suka kwace a hannunsa da karfin binidaga. A ranar 26 ga watan Yulin wannan shekara ta 2023 da muke ciki ne dai, sojoji suka yi wa Bazoum juyin mulki suka kuma tsare shi tare da iyalansa. Juyin mulkin sojojin na Jamhuriyar Nijar dai ya sha suka daga al'ummomin kasa da kasa, tare kuma da janyo jerin takunkumai ga kasar da ke zaman guda cikin mafiya talauci a duniya.