1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Batutuwan Afirka da suka dauki hankalin jaridun Jamus

Usman Shehu Usman ZMA
May 3, 2024

Zaben 'yan majalisa aTogo da matakin Burkina Faso na rufe wasu kafafen yada labaru da mummuman ambaliyar ruwa a kasashen gabashin Afirka su ne jaridun suka mayar da hankali a kai.

https://p.dw.com/p/4fTlT
Ambaliya a KenyaHoto: Thomas Mukoya/REUTERS

Zamu fara sharhunan jaridun na Jamus kann Afirka ne da siyasar yammacin Afirka. Inda die Tageszeitung, ta ce Tsohuwar gwamnati na neman sabon mulki. Wannan shi ne labarin jaridar die Tageszeitung. Jaridar na magana ne kan kasar Togo, inda a Litinin farkon makon nan aka yi zaben yan majalisar dokoki, wadanda su ne kuma za su zabi shugaban kasa bisa sabon tsarin mulkin kasar wanda ake sauyawa kamar tufafi. Tun kimanin shekaru 60 iyali guda ke mulkin 'yar karamar kasar da ke a yammacin Afirka.

Kuma a bana sabon salon da shugaba Faure Yadema ya bullo da shi don ci gaba da mulki, shi ne cewar daga yanzu 'yan majalisar dokoki ne za su zabi shugaban kasa kuma wai wa'adi daya kawai zai yi. Batun da ya jawo zanga-zangr da ta kai ga mutuwar mutane da yawa sakamkon amfani da karfin jami'an tsaro.

Togo | Wahlen
Zaben TogoHoto: Emile Kouton/AFP

Sai jaridar die Spiegel wace ta ce Burkina Faso ta dau mataki na rufe kafafen yada labarai musamman na bagaren radio. Jaridar ta kara da cewa hukumomin soja a Burkina Faso sun fusata bayan yada labarin wani zargi da aka yi wa sojojin kasar na aikata kisan kiyashi. Burkina Faso ta dakatar da watsa shirin gidajen radio na BBC da VOA a hadi da tashar DW a kasar. A cewar kungiyar kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch, akwai shaidu da ke nuna babban tabbacin hannun sojojin gwamnati a kisan fararen hula, cikin kokarin da kasar ke yi na yaki da ta'addanci.

Wannan kuwa labari ne da akasarin kafafen yada labaran duniya suka dauka, abinda ya haddasa fushin gwamnatin wace ke ganin ana yi mata katsalandar cikin gida. Ba dai shi ne karon farko da ake tuhumar sojan Burkina Faso da aikata kisan fararen hula musamman tun bayan da sojoji suka kwace mulkin kasar ba.

Burkina Faso | France 24 abgeschaltet
Toshe kafofin yada labaru a Burkina FasoHoto: Olympia De Maismont/AFP

Ita kuwa jaridar FAZ ta yi sharhi ne da ke cewar a kasashen Kenya da Tanzaniya daruruwan mutane suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan sama da ya haddasa asarar dukiya. Jaridar ta ci gaba da cewa, faruwar ibtala'in ba wai matsalar sauyin yanayi ba ne kawai. Damina ce mai karfin gaske ake yi cikin kwanakin nan a gabar ruwayen gabashin Afirka. Kama daga tekun Indiya har izuwa cikin dajin Kwango.

Ruwna sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta samu cikin kwanaki da makwannin da suka gabata sun haddasa ballewar madatsun ruwa a yankin, wanda kuma ya haifar da ambaliyar ruwa cikin garuruwa yana rusa gidaje.

Sai Jaridar Neuer Zürcherzeitung, wace a sharhinta ta ce mallakar arzikin karkashin kasa yana iya zama koma baya ga kasa, ya danganta ne kawai a wace kasa ko yanki wannan arzikin yake.

Überschwemmung Daressalam Tansania
Ambaliya a Daressalam-TansaniyaHoto: Amas Eric/DW

Jaridar na misali da kasar Sudan wace a yanzu ta dau lokaci ana yakin basasa mai muni, kuma an kasa shawo kan lamarin, bisa irin hannayen da kasashen masu fada aji ke da shi a cikin rikicin. Inda yanzu jaridar ta ce kusan duk inda ake rigima ko yaki kusan dole za ka samu hannun Amurka da Chaina da Faransa da Ingala, kuma dukkansu ko wace arzikin ma'adinai da kuma biyan bukatunta ne ya janyo hakan.

A kasar Sudan ko wane bangare cikin masu yakin na samun tallafi daga daya cikin manyan kasashen duniya, yayin da su kasashen da ke da karfin masana'antu ke kwashe arzikin Sudan walau na ma'adinai ko kuma karban kudin gwamnati don sayar mata makamai, su kuwa talakawan kasar Sudan sun ke mutuwa kuma babu alamar ranar kawo karshen lamarin.