1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila da Hamas za su sake hawa kan teburin sulhu

May 4, 2024

Tawagar Hamas za ta isa birnin Alkahiran Masar domin a ci gaba da tattauna yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

https://p.dw.com/p/4fV0i
Isra'ila da Hamas za su sake hawa kan teburin sulhu
Isra'ila da Hamas za su sake hawa kan teburin sulhuHoto: Amr Abdallah Dalsh/REUTERS

Kasashen da ke shiga tsakani a rikicin kungiyar Hamas da Isra'ila na jiran tsamanin jin martani daga kungiyar kan daftarin yarjejeniyar da Isra'ila ta mika na dakatar da yakin na tsawon kwanaki 40 da kuma musayar fursunoni.

A jiya Juma'a, sakataren harkokin wajen Amirka, Antony Blinken ya ce abun da ke tsakanin al'umma Gaza da kuma wannan yarjejeniya shi ne kungiyar ta Hamas.

Karin bayani: An shirya bude taron sulhun Masar kan yakin Gaza

An dai shafe tsawon watanni tattaunawar na tafiyar hawainiya saboda bukatar Hamas na tsagaita bude wuta mai dorewa da kuma alwashin da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu na murkushe sauran mayakan kungiyar a Rafah.

Kungiyoyin agaji na kasa da kasa da kuma Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da rokon Isra'ila da ta dakatar da dukannin hare-hare kan birnin Rafa inda mutane fiye da miliyan 1.2 ke samun mafaka.