1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haiti: Rantsar sabuwar gwamnatin rikon kwarya

April 25, 2024

Za a rantsar da gwamnatin rikon kwarya a Haiti yayin da tashe-tashen hankula a kasar ya haifar da kafa gwamnatin wucin gadi.

https://p.dw.com/p/4fA0Y
Za a rantsar da gwamnatin rikon kwarya a Haiti
Za a rantsar da gwamnatin rikon kwarya a Haiti Hoto: H. Tschanz-Hofmann/IMAGO

Za a gudanar da bikin rantsar da sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Haiti a offishin Firanministan kasar inda ake sa ran gwamnatin mai mambobi 9 ta cike gibin shugabancin kasar. Kasar ta Haiti dai ta fada cikin rikicin siyasa ne bayan da kungiyoyin miyagu suka far wa babban birnin kasar Port-au-prince tare da mika bukata ga Firanminista Ariel Henry da ya yi murabus.

Karin bayani: Jagororin siyasar Haiti sun amince da kafa gwamnatin rikon kwarya

Ana dai ganin akwai jan aiki a gaban sabuwar gwamnatin rikon kwaryar ciki kuwa har da shirya babban zabe a watan Fabarairun 2026 a kasar da rabon da ta shirya zabe tun a shekarar 2016.