1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar Hidaya za ta tunkari Kenya da Tanzaniya

May 4, 2024

Mahaukaciyar guguwar Hidaya za ta tunkari kasashen Kenya da Tanzaniya ne a daidai lokacin da suke fama da iftila'in ambaliyar ruwa.

https://p.dw.com/p/4fV0n
Kasashen Kenya da Tanzaniya sun fuskanci iftila'in ambaliyar ruwa a baya-bayan nan
Kasashen Kenya da Tanzaniya sun fuskanci iftila'in ambaliyar ruwa a baya-bayan nanHoto: Feisal Omar/REUTERS

Kasashen Kenya da Tanzaniya sun fara shirin ko-ta-kwana yayin da ake hasashen mahaukaciyar guguwa ta Hidaya ta tunkara kasashen a wannan Asabar din. Ana sa ran guguwar za ta haifar da kadawar iska mai karfi da kuma saukar mamakon ruwan sama.

Kawo yanzu, gwamnatin Kenya ta kwashe mutanen da ke zaune kusa da madatsun ruwa kimanin 170 da kuma wadanda ke gabar teku. Mahaukaciyar guguwar dai na tunkarar kasashen ne makwanni bayan da suka fuskanci mummunar ambaliyar ruwa.

Alkalumma sun yi nuni da cewa, fiye da mutane 200 ne suka mutu a Kenya yayin da wasu dubu 165 suka rasa matsugannunsu ko ba ya ga 155 suka gamu da ajalinsu a Tanzaniya sakamakon iftila'in na ambaliyar ruwa da kuma zaftarewar kasa.