1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil: Ambaliyar ruwa ta yi sanadin gomman rayuka

May 4, 2024

A Brazil mutane 40 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 68 suka bace sakamakon ambaliyar ruwan a kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/4fVSi
Ambaliyar ruwa ta mamaye anguwanni fiye 265 a jihar Rio Grande do Sul da ke Brazil
Ambaliyar ruwa ta mamaye anguwanni fiye 265 a jihar Rio Grande do Sul da ke BrazilHoto: Diego Vara/REUTERS

Hukumomi na cewa fiye da mutane 24,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon iftila'in ya shafi anguwanni fiye 265 a jihar Rio Grande do Sul. Shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva ya bayyana iftila'in ambaliyar ruwa ta wannan lokacin a matsayin mafi muni a tarihin kasar. An tura da jami'an agaji a fiye da 2,000 zuwa sassa daban-daban domin kai dauki ga jama'a. Kawo yanzu dai an ceto 8,000. Tun a ranar Litinin ce ake tafka ruwan sama wanda ya haifar da iftila'in da ya mamaye gidaje da lalata hanyoyi da kuma gadoji.